Fitaccen dan wasan kungiyar Barcelona da kasar Sifaniya, Andres Iniesta, ya bayyana jingine takalmansa daga buga wasan kwallon kafa ya na da shekaru 40 a Duniya.
Tsohon dan wasan tsakiyar Barcelona ya kasance ba tare da wata kungiya ba har tsawon watanni bayan ya bar kungiyarsa ta baya-bayan nan, Emirates FC Club.
- Uwargidan Gwamnan Kebbi Ta Raba Babura 42 Da Motoci 2 Domin Inganta Sa ido Kan Cutar Tarin Fuka
- NUJ Ta Taya Gwamnan Kebbi Da Nijeriya Murnar Cika Shekaru 64 Da Samun ‘Yancin Kai
Iniesta ya na daya daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Sifaniya, shi ne ya ci kwallon da ta bai wa Sifaniya nasara a wasan karshe na gasar cin kofin Duniya a shekarar 2010 wanda kuma shi ne kofin Duniya na farko da kasar ta taba lashewa.
Ya kuma kasance jigon nasarar da suka samu a gasar Euro 2008 da 2012, ya buga wa kasarsa wasanni 131, ya ci kwallaye 14, shi ne a matsayi na biyar a jerin ‘yan wasan da suka fi kowa taka leda ga kasar bayan Sergio Ramos da Iker Casillas da Sergio Busquets da Xavi Hernandez.
Iniesta na daga cikin yan wasan da suka taka rawa har Barcelona ta lashe kofuna uku rigis(treble)- a shekarar 2009 da kuma 2015, ya lashe kofuna hudu na gasar cin kofin zakarun Turai, La Liga 9, Copa del Rey 6, Club World Cups 3, da kuma Supercup 10 a Barcelona.
Iniesta ya buga wasanni 674 gaba daya a Barcelona, inda ya zura kwallaye 57 sannan ya taimaka aka samu nasara sau 135, ya fara buga wa kungiyar kwallo a 2002 ya kuma barta a shekarar 2018.
A kididdigar duka, rayuwar kwallonsa Iniesta ya buga wasanni 1,016, ya zura kwallaye 107 sannan ya taimaka an an samu nasara sau 191.