Ofishin jakadancin Isra’ila a Nijeriya ya kaddamar da wani shiri mai suna i-FAIR, wanda zai samarwa ‘yan Nijeriya sama da miliyan daya ayyukan yi.
Da yake magana a taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis gabanin kaddamar da shirin na uku, Jakadan kasar Isra’ila a Nijeriya, Michael Freeman, ya ce shirin zai fi amfanar matasan Nijeriya.
“Mako daya da ya gabata, an kaddamar da shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban Nijeriya, daya daga cikin muhimman abubuwan da ya ayyana zai fi ba muhimmanci a mulkinsa a ranar rantsar da shi, shi ne ingantawa da karfafa tattalin arzikin Nijeriya.
“Ya yi magana musamman kan wasu manufofin inganta saka hannun jari a Nijeriya da kuma samar da ayyukan yi sama da miliyan daya a bangaren tattalin arziki na dijital.
“Shirin i-FAIR na daya daga cikin shirye-shiryen da za su taimaka wajen samar da ayyukan yi miliyan daya a cikin tattalin arzikin dijitali,” inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp