Wata majiya ta ce, kimanin masunta 26 ne ‘yan kungiyar ta’addanci ta ISWAP suka kashe a garin Gamborun Ngala da ke karamar hukumar Ngala a cikin jihar Borno.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, an kashe masuntan ne a ranar Laraba a yayin da suke kamun Kifi da kuma saro itacen girki a kauyen Mukdolo kimanin kilomita 19 da garin Dikwa.
Bayanan da aka samu daga mai fashin baki kan lamarin tsaro da tayar da kayar baya a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ya ce, ‘yan ta’addar sun kai harin ne akan babura, inda suka bude wa masuntan wuta.
Majiyar ta ce, tara daga cikin masuntan sun tsira, Uku daga cikinsu sun tsira dauke da harbin alburusai a jikinsu.
Majiyar ta ce, daga baya dakarun soji sun kai musu dauki inda suka gano gawarwarkin masuntan, an yi musu jana’iza a ranar alhamis kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp