Yayin da yake zantawa da kafafen yada labaran Amurka kwanan nan, mataimakin shugaban kasar Amurka, J. D. Vance, ya yi wani furuci da ya bayyana rashin hankalinsa, inda ya ce Sinawa kauyawa ne, furucin da ya gamu da babbar dariya daga masu amfani da shafukan sada zumunta na kasashen waje, inda a cewarsu, karamin sani kukumi ne ga Vance.
Rashin sani na Vance, ya nuna cewa bai fahimci kasar Sin ba, kuma bai fahimci manyan sauye-sauyen da kasar ta samu a fannin ci gaba ba, kai, bai ma fahimci yadda duk duniya take samun muhimman sauye-sauye ba. Ba shakka, bai fahimta ba, ko kuma mu ce ba ya son ya amince cewa akwai tarin matsalolin dake tattare da tsarin siyasar Amurka, kana, ba ya son ya yarda cewa, babakeren Amurka na kara rugujewa.
Ya kamata ’yan siyasar Amurka, ciki har da J. D. Vance, su bude idonsu su ga wannan duniya don su gane cewa, ka’idar kasarsu ba ka’ida ce ta duk duniya ba, kuma bai kamata babakeren Amurka ya yi wani tasiri ga duniya ba. Yayin da suke amfani da batun karin harajin fito don su saka duniya cikin halin-kaka-nika yi, ya kamata su san cewa, irin rashin sani da rashin mutunci da kuma tsageranci na Amurka, na kara janyo tabarbarewar babakerenta. (Murtala Zhang)














