A jiya Jumma’a, babban jakadan kasar Sin na kujerar din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya, Fu Cong ya bayyana cewa, har yanzu dai halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (DRC) na ci gaba da tabarbarewa, kuma kasar Sin na fatan dukkan bangarorin da abin ya shafa su yi biyayya ga kiraye-kirayen da kasashen duniya da kwamitin sulhu na MDD ke yi musu, ta hanyar gaggauta dakatar da duk wani tashin hankali, da kuma kaurace wa duk wani mataki da ka iya ta’azzara zaman dar-dar.
A yayin da yake jawabi a kan kuri’ar daftarin kwamitin sulhun game da halin da ake ciki a kasar ta DRC, Jakadan ya ce rikicin da ya barke a baya-bayan nan a gabashin kasar ta DRC wanda aka dauki tsawon makwanni ana tafkawa, duk ya addabi kasashen duniya.
Fu ya kara da cewa, bayan kungiyar ’yan tawaye ta M23 ta kwace birnin Goma, wanda ya saba wa kiran da kasashen duniya da na shiyya-shiyya suka yi na tsagaita bude wuta, da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kashin kanta da ta yi, ta sake kame birnin Bukavu da sauran wurare, lamarin da ya kara rura wutar rikicin a gabashin DRC, tare da kara haifar da fargabar fantsamar rikicin zuwa na yanki baki daya.
Jakadan ya kuma ce, kudurin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi ba da jimawa ba, ya bukaci kungiyar ta M23 da ta gaggauta tsagaita wuta tare da ficewa daga yankunan da ta mamaye. Wannan kuma ya yi dai-dai da fatan kasashen duniya da kasashen yankin na ganin an tsagaita bude wuta da kuma dakatar da rikicin, sannan kuma wani mataki ne da kwamitin sulhun ya dauka don sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Mista Fu ya nanata cewa, kasar Sin na nuna goyon baya sosai ga warware matsalolin Afirka ta hanyar da ta dace da nahiyar, yana mai jaddada cewa, kamata ya yi a tsara kudurorin kwamitin sulhu na MDD da za su taimaka wa tafiyar da harkokin shiyya-shiyya, don samar da daidaito da kokarin sulhu a matakin shiyya-shiyya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)