Jakadan Sin dake kasar Nijeriya Cui Jianchun ya gana da shugaban jam’iyyar APC ta kasar, Abdullahi Adamu, a jiya.
A yayin ganawar, Cui ya bayyana cewa, Sin da Nijeriya suna mu’amala da hadin gwiwa da juna a fannoni daban daban a shekarun baya-baya nan, kuma sun yi imani da juna a fannin siyasa, da samun nasarori da dama kan hadin gwiwarsu.
Ya ce Sin tana dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwar dake tsakanin jam’iyyun kasashen biyu, kuma tana son kara yin mu’amala da jam’iyyar dake mulkin kasar Nijeriya don sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin jam’iyyun kasashen biyu, da taimakawa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin masana’antu, da aikin gona, da hada-hadar kudi da sauransu, ta yadda za a inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, malam Adamu ya bayyana cewa, ana sada zumunta a tsakanin Nijeriya da Sin, kuma Sin ta bayar da gudummawa wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Nijeriya.
Ya ce jam’iyyar APC na dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana son hada hannu da kasar Sin wajen zurfafa imanin siyasa, da sa kaimi ga yin mu’amala da juna a harkokin kasa, don inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. (Zainab)