• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jakadan Sin Dake Najeriya Ya Gana Da Shugaban Jam’iyyar Mai Mulkin Kasar Abdullahi Adamu

byCMG Hausa
3 years ago
Sin

Kwanan baya, jakadan kasar Sin dake Najeriya Cui Jianchun, ya gana da shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasar Sanata Abdullahi Adamu.

A yayin ganawar, Cui Jianchun ya bayyana cewa, babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, wani muhimmin lamari ne a tarihin harkokin siyasar jam’iyyar da jama’ar kasar Sin.

  • Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Yi Cikakken Kokarin Shawo Kan Illar Da Ke Tattare Da Yanayin Da Ake Ciki Game Da Rikicin Rasha Da Ukraine

A cikin shekaru kusan 10 da suka gabata, karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kasar Sin ta cimma nasarar gina al’umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, kuma ta samu sakamako mai kyau wajen kawar da talauci, da yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da yaki da annobar COVID-19 da dai sauransu.

Ya ce jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana son zurfafa musanyar fasahohin da ta samu a harkokin mulkin kasa tare da jam’iyyar APC, da sa kaimi ga hakikanin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kiyaye daidaito da adalci a duniya tare, da hada karfi don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a cikin sabon zamani.

A nasa bangaren, Sanata Adamu ya taya murnar gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 cikin nasara, ya kuma yaba wa mu’amalar dake tsakanin jam’iyyun biyu, da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ya kuma jaddada cewa, kasarsa tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Baya ga haka, ya bayyana aniyarsa ta kara koyo daga fasahohin da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta samu wajen cimma nasara, da tabbatar da sabon ra’ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, don ci gaba da samun sabbin nasarori, ta yadda jama’ar kasashen biyu za su amfana. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Kasar Nan Kawanya – TY Danjuma 

‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Kasar Nan Kawanya – TY Danjuma 

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version