Ran 1 ga watan nan na Satumba, hukumar tuntubar kasashen waje ta kwamitin tsakiyar JKS, da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, da jam’iyyar APC mai mulkin kasar, sun shirya gabatar da ajin horas da mambobin jam’iyyar APC ta yanar gizo da kuma ta zahiri, bisa taken “Kara karfin jami’iyya mai mulkin kasar don ba da jagoranci”.
Mataimaki ga ministan hukumar Li Mingxiang, ya halarci bikin bude zaman ta kafar bidiyo tare da ba da jawabi. Kaza lika shi ma jakadan Sin dake kasar Cui Jianchun ya ba da jawabinsa. Sai kuma manyan jami’ai fiye da 30 na jam’iyyar APC, ciki har da mataimakin darektan jam’iyyar Festus Fuanter, duk sun halarci bikin.
A jawabinsa, Li Mingxiang ya nuna cewa, Sin na fatan hadin kai da Najeriya, da mutunta muradunsu masu tushe, da abubuwan da suke jawo hankalinsu, don tabbatar da shawarwarin raya duniya baki daya, da shawarwarin ba da tabbaci ga tsaron duniya, da gaggauta kafa kyakkyawar makomar al’ummar Sin da Afrika ta bai daya a sabon zamani.
A nasa bangare, mataimakin darektan jam’iyyar APC Festus Fuanter ya nuna cewa, JKS wata jam’iyya ce mai karfin jagoranci dake da tarihi shekaru 101, kuma tana da tasiri matuka a duniya, APC jami’iyya ce da ba ta jima da kafuwa ba.
Ya ce al’ummar Sinawa sun samu nasarar yaki da talauci, da tinkarar COVID-19, da farfado da tattalin arzikinta, karkashin jagorancin shugaban kasar Xi Jinping, abin da ya kamata Najeriya ta yi koyi da shi.
Ya ce Najeriya za ta ci gaba da kara mu’ammala da bangaren Sin, don koyon fasahohin JKS wajen gudanar da harkokin kasa. (Amina Xu)