Jakadan kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva Chen Xu, ya yi kira ga ofishin kare hakkin bil adama na MDD ko OHCHR, da ya rika martaba zabin kasashen duniya game da tafarkin da suka zaba, na bunkasa kare hakkin bil adama daidai da yanayin kasashen.
Chen Xu ya yi kiran ne a jiya Talata, a madadin wasu tawagogi na kasashe sama da 30, yayin zama na 51 na majalissar kare hakkin bil adama. Yana mai cewa, amincewa da juna, na da babban tasiri wajen gudanar da hadin gwiwa tsakanin ofishin OHCHR da kasashe mambobinsa.
Chen ya kara da cewa, sake bullar annobar COVID-19 da ake gani a yanzu, na nuni ga gazawar sassan masu ruwa da tsaki, na ingiza ci gaban tattalin arziki, da kyautata zamantakewa da raya al’adun al’umma, da tallafawa damarsu ta samun ci gaba, da damar cin cikakkiyar gajiya daga rayuwa ta fannin lafiyar jiki da tunani.
Ya ce, “Kiranmu ga OHCHR shi ne ya dora muhimmancin gaske, ga samar da karin albarkatu don gudanar da wannan aiki, tare da kawar da rashin daidaito a ayyukansa, ya kuma taimakawa kasashe musamman masu tasowa, wajen shawo kan kalubalolin yaki da annoba, da cimma nasarar raya tattalin arziki, zamantakewa da wanzar da ci gaba. (Saminu Alhassan)