Jakadu daga kasashe 25 da suka hada da Dominica, Myanmar, Iran, Samoa da Surinam, sun ce ba su ga abin da ake kira “aikin tilastawa” da “kisan kare dangi” a yankin Uygur na Xinjiang mai cin gashin kansa na arewa maso yammacin kasar Sin ba, bayan ziyarar da suka kai a can daga ranar 31 ga watan Yuli zuwa 4 ga Agusta, bisa gayyatar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi musu.
Wakilan sun je babban birnin yankin Urumqi da yankunan Kashgar da Aksu, inda suka ziyarci tsohon birnin na Kashgar, da masallatai, da cibiyoyin nazarin Musulunci, da gidajen adana kayayyakin tarihi, da kamfanonin aikin gona.
A cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin a jiya Laraba, tawagar ta shaida yadda al’ummar yankin ke gudanar da rayuwar yau da kullum, da ganin al’adu daban-daban, da kuma lura da yadda ake samun bunkasuwar tattalin arzikin cikin gida, da kokarin da gwamnatin kasar Sin ke yi na yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi. (Mai fassara: Yahaya)