Manufar sanya muradun Amurka gaba da komai, tana rikidewa zuwa karin cin zali ta hanyar kakaba haraji. Barazanar sabuwar gwamnatin Amurka ta kakaba haraji kan kasar Sin domin daukewa kasar Mexico haraji, ya ja hankalin al’ummar duniya.
Wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar tsakanin masu amfani da intanet a duniya ya nuna cewa, kaso 70.4 na wadanda suka bayar da amsa sun yi imanin cewa, shirin Mexico na sanya haraji kan kayayyakin Sin, ya samo asali ne daga matsin da manufofin haraji na Amurka suka haifar, wanda ke da nufin kawar da mummunan tasirin harajin Amurkar a kanta
Hakika tun bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta fara aiki, ba a tsagaita cin zali a bangaren tattalin arziki bisa fakewa da sanya muradun Amurka gaba da komai ba. Kaso 76.4 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana damuwar cewa, idan Mexico ta amince da matsin Amurka ta kakaba haraji kan sauran kasashe, za ta bayar da mummunan misali ga kasa da kasa, lamarin da zai kara hargitsa tsarin cinikayya na duniya.
Baya ga haka, wasu kaso 73 sun soki Amurka da cewa, tana amfani da batun haraji wajen matsawa sauran kasashe ta fuskar tattalin arzikin, inda take ta’azzara mummunan tasirinsa a harkokin cinikayya na duniya da kawo tsaiko ga tsarin cinikayya da daidaiton tsarin samar da kayayyaki. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp