Jami’ai daga sassan kasa da kasa sun jinjinawa manufar gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama da kasar Sin ta gabatar, yayin da suke halartar wani taron kasa da kasa, inda suka yi musayar ra’ayoyi a kan matakan farfadowa bayan annobar COVID-19, da muhallin halittun duniya, da musaya tsakanin mabanbantan wayewar kai, da cudanyar sassa daban daban da dai sauran su.
Taron wanda ya gudana a Larabar nan, a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, ya hallara jami’an gwamnatoci daga nahiyoyin duniya 3, da jagororin hukumomin kasa da kasa da masana.
Da yake tsokaci cikin jawabin sa na bude taron da ya gudana a babban dakin taruwar jama’a, mamba a ofishin harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban sashen yada bayanai na kwamitin Li Shulei, ya yi karin haske game da muhimmancin wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya, yana mai kira da a yayata manufar hadin gwiwar cimma moriyar juna da zuciya mai rungumar kowa.
Li Shulei ya kara da cewa, kasar Sin za ta nacewa alkawarin da ta yi na bunkasuwa cikin lumana, da kara ba da gudummawa wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama. (Saminu Alhassa)