Jami’an kasar Sin da na Tarayyar Afirka (AU) sun bayyana cewa, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka na kara habaka, inda aka samu karuwar kasuwanci da kashi 6 cikin dari a mizanin shekara-shekara wanda kudinsa ya kai dalar Amurka biliyan 295 a shekarar 2024.
A cewar jakadan tawagar wakilan kasar Sin a kungiyar AU, Hu Changchun, kasar Sin ta ci gaba da zama babbar abokiyar cinikin Afirka a tsawon shekaru 15 a jere, inda kusan rabin kasashen yankin na Afirka suka samu habakar cinikayya da Sin da fiye da kashi 10 a bara.
- Xi: Daukar Matsayar Kashin Kai Da Danniya Ba Za Su Taba Samun Goyon Bayan Al’umma Ba
- APC Ta Gaza Gudanar Da Taron NEC Cikin Shekaru Biyu – PDP Ta Zarge Su
Hu ya bayyana hakan ne a yayin wani taron kara wa juna sani kan tattalin arziki da hadin gwiwar kasuwanci tsakanin Sin da Afirka, a ranar Larabar da ta gabata, wanda tawagar kasar Sin da kungiyar ma’aikatan AU suka shirya a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta soke harajin kwastam baki daya ga dukkan kasashe marasa karfi, inda kasashe 33 na Afirka ke cikin wadanda suka ci gajiyar hakan, kana ya jaddada cewa, kyawawan sakamako na hakika da ake samu suna bayyana cikakkiyar aniyar kasar Sin da babbar murya wajen fadada bude kofarta, da ba da damammakin samun ci gaba ga kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa.
Da yake jawabi a taron, shugaban ma’aikatan hukumar AU, Mohamed El-Amine Souef, ya yaba da goyon bayan da kasar Sin ta dade tana bai wa Afirka, wanda ya samo asali tun a shekarun 1960 da 1970 lokacin da kasashen Afirka da dama suka samu ‘yancin kai.
Souef ya ce, gudummawar da Sin ta bayar ga ci gaban Afirka, da ta kunshi gina manyan ababen more rayuwa, da tallafa wa fannonin kiwon lafiya da tsaro, da horar da manyan jami’an sojin yankin, abar yabawa ce. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp