Wasu jami’an kasar Habasha, sun ce Sin ta cimma manyan nasarori a fannin raya tattalin arziki na dijital, wanda hakan ya zamo abun misali wajen bunkasa sauyi zuwa ga ci gaba na dijital a Habasha.
Jami’an sun bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin kaddamar da makon raya ci gaba na dijital karo na farko a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar, wanda aka yiwa take da “Tattara karfi don bunkasa ci gaba na dijital a Habasha”.
Da yake tsokaci kan hakan, babban mashawarci a ma’aikatar kirkire-kirkire da raya fasaha a kasar Habasha Abiyot Bayou, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, akwai darussa da dama da Habasha za ta iya koya daga sauyi da Sin ta samu ta fuskar ci gaba na dijital, ciki har da kwazon siyasa, da cin gajiya daga ilimin ‘yan kasa, da sanin makamar aiki, da ma aiki tukuru wajen ingiza cin gajiyar fasahohin dijital a kasar dake gabashin Afirka. (Mai fassara: Saminu Alhassan)