Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, He Yadong, ya sanar da cewa, bisa amincewar kasashen Sin da Rasha, za a gudanar da taron karo na 28 na kwamitin kula da tattaunawa tsakanin firaministocin Sin da Rasha a birnin Moscow, babban birnin kasar Rasha, daga ranar 19 zuwa 20 ga watan Agusta. Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ne zai jagoranci taron tare da mataimakin firaministan Rasha Dmitry Chernyshenko.(Safiyah Ma)