Jami’an tsaro da ‘yan banga sun yi nasarar kama ɓarayin kayayyakin wutar lantarki da suka yi kokarin katse turakun wutar na T297, T298 da T299 da ke kan hanyar Mando zuwa Jos a Kaduna.
Jami’in Hulda da Jama’a na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN), Ndidi Mbah, a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ya ce barayin sun cire wasu muhimman abubuwan turakun Lantarkin, wanda hakan ka iya kawo cikas ga kai wutar zuwa inda ya dace.
Sanarwar, ta jinjinawa Jami’an tsaron, da ‘yan banga da al’ummar yankin kan matakin da suka dauka, wanda ya kai ga cafke barayin, ta kara da cewa, wadanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda a Saminaka, Kaduna, inda ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.