A yau Talata, 26 ga Agusta, 2025, jami’an tsaron Nijeriya sun samu damar kubutar da mutum 128 daga hannun ‘yan bindiga a Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.
An gabatar da mutanen da aka kuɓutar a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, wanda ya bayyana lamarin a matsayin “babbar nasara a yaƙin da ake yi da rashin tsaro a Nijeriya.”
- Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin
- Saka Zai Yi Jinyar Makonni 4 Sakamakon Rauni Da Ya Samu A Wasan Leeds
Yayin da yake jawabi a gaban waɗanda aka ceto, Ribadu ya ce aikin bai tsaya kan kuɓutar da mutanen da aka kama kawai ba, har ma ya haɗa da lura da yanayin lafiyarsu da kuma tabbatar da an haɗa su da iyalansu cikin aminci.
Ribadu ya yaba da jajircewar sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, yana mai cewa, wannan wata nasara ce da za a yi alfahari da ita a tarihin yaki da ta’addanci.
A Guji Siyasantar da Tsaro
Sai dai Ribadu ya gargadi shugabannin siyasa da masu rike da madafun iko da su guji siyasantar da al’amuran tsaro, yana mai cewa:
“Wannan ƙalubale na gama gari ne, ba wai na shugabanni kaɗai ba. Domin haka nake kira ga al’umma da shugabanni su daina siyasantar da tsaro.”
Ribadu ya ƙara da cewa, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin magance barazanar tsaro tare da kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp