A wani hari da tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa suka kai, sun yi nasarar kashe kasurgumin jagoran ‘yan bindiga mai suna Baƙo-baƙo tare da mayakansa a dajin Batsari a karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.
Harin wanda aka gudanar da yammaci, ya hada da sojojin Nijeriya, ‘yansanda, jami’an tsaron farin kaya na NSCDC, da kuma ‘yan sakai (CWC).
- An Kashe ‘Yan Boko Haram Da Dama A Harin Da Suka Kai A Fadar Shugaban Kasar Chadi
- Tinubu Ya bayar Da Umarnin Bincike Kan Harin Da Boko Haram Ta Kai Wa Sansanin Sojoji A Borno
Baƙo-baƙo, wanda ya yi kaurin suna wajen jagorantar munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da ta’addancin al’umma a fadin jihar Katsina, ya kasance cikin ƙomar jami’an tsaro tuntuni.
Kawar da shi ya nuna wani gagarumin ci gaba a yaƙin da ake yi da ‘yan ta’adda a yankin.
Wani shugaban al’ummar yankin ya ce, “Wannan babbar nasara ce ga al’ummarmu. Muna matukar godiya da kokari da sadaukarwar da sojojin suka yi wajen dawo da zaman lafiya a yankinmu.”