Jami’an tsaro a Nijeriya sun kashe ‘yan fashin daji takwas tare da Æ™wace babura yayin wani samame da suka kai a yankin Chikun da Birnin Gwari na Jihar Kaduna, a cewar gwamnatin jihar.
BBC ta rawaito cewa, Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya ce dakarun rundunar rundunar haÉ—in gwiwa na Operation Forest Sanity ne suka Æ™addamar wa ‘yan bindigar cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a.
“Dakarun sun gwabza da ‘yan fashin kuma suka kashe takwas daga cikinsu, sannan suka Æ™wace babura huÉ—u da wayoyin hannu a samamen farko,” in ji shi.
Jami’an tsaron sun sake karawa da ‘yan bindigar a karo na biyu kuma suka Æ™wace babur biyu.
A gefe guda kuma, dakarun sun yi nasarar kashe wasu ‘yan fashi biyu a yankin Sabon Birni da Maidaro da Dogon Dawa, duka a Jihar ta Kaduna.
A wannan karon ma, jami’an tsaro sun Æ™wace bindiga Æ™irar AK-47 da kuma harsasai da dama.