Darektar gasar wasannin daliban jami’o’in kasa da kasa dake gudana a birnin Chengdu na kasar Sin Zhao Jing, ta shaidawa taron manema labarai cewa, tawagogi daban-daban dake halartar gasar, sun yaba kan abubuwan da aka tanada a gasar.
Ta ce, wannan ba kokarin kwamitin shirya gasar ba ne kadai, har ma da goyon bayan da gasar wasannin daliban jami’o’in kasa da kasa ta Chengdu kanta ta bayar, da kuma yadda aka amince birnin Chengdu ya karbi bakuncin gasar.”
Jami’ar ta ce, ta ga rubuce-rubuce da dama da tawagogi daban-daban dake halartar gasar suka wallafa a yanar gizo game da abubuwan da suka gani a titunan Chengdu. Tana mai cewa ba wai kawai sun zo don gasar ba ce, har ma don kara fahimtar birnin. Kuma wannan a cewarta shi ne ainihin muhimmancin gudanar da wannan gasa.
Bayan da ta halarci irin wadannan gasanni da dama, Zhao ta ce ta yi imanin cewa, babban dalilin samun nasarar gasar ta Chengdu, shi ne kyakkyawan tsari da tallafi na musamman da aka samu.
Ta kara da cewa, gamayyar kungiyoyin wasannin motsa jiki ta jami’o’in Sin, ta samu cikakken goyon baya daga gwamnati da ma daukacin jama’ar birnin. (Ibrahim)