Jami’ar Franco-British International University a Kaduna, jami’a ce irinta ta farko a Nijeriya da take da salon koyarwa na Birtaniya da Faransa, ta shirya soma fara ayyukan ilimi a watan Oktoban 2024.
Hakan ya fito ne a wata tattaunawa da shugaban jami’ar, Farfesa Abdullahi Muhammad Sabo da manema labarai a ranar Litinin.
- Gwamnati Ta Janye Dokar Hana Fita A Kaduna Da Zariya
- Yadda Mahara Suka Jefa Bam A Ofishin Jami’yyar APP A Ribas
A cewar shugaban jami’ar, jami’ar za ta fara ne da makarantu uku, wato; makarantun Kwamfuta (Computing), Jinya (Nursing), da Kimiyyar Lafiya (Health Sciences).
Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne ya kafa Jami’ar Franco-British International University, wanda kuma shi ne ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da ta Nijer (MAAUN) da kuma Jami’ar Canada da ke Abuja.
Har ila yau, wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Gwarzo, a wata sanarwa da ya fitar a lokacin ziyarar shugaban jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), Farfesa Armayau Hamisu Bichi, ya nanata kishinsa da jajircewarsa kan harkar ilimi, inda ya ce zai bai wa fannin dukkanin gudummawar da ya kamata.
Ya lurantar da cewa a Nijeriya, “Jami’ar Franco-British International University (FBI) wani yunƙuri ne na fitar da ingantaccen ilimi a Afirka.”
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta ba Jami’ar Franco-British International lasisin aiki a shekarar 2023 tare da Jami’ar Canada ta Nijeriya, wacce kuma ke cikin rukunin jami’o’in MAAUN.
“An san ni kan ilimi kuma zan ci gaba da jajircewa akan hakan. Mun yi shi a jamhuriyyar Nijar da Kano. Mun kafa ruhin ɗabi’a mai kyau da ingantaccen ilimi a tsakanin ɗalibanmu da ma’aikatanmu.
“Za mu tabbatar da inganci, tarbiyya, da kuma da’a a tsakanin dalibai da ma’aikatan Jami’ar Franco-British International University kamar yadda muke yi a Kano da Nijar,” in ji Farfesa Gwarzo.