Jami’ar kimiyya ta gwamnati tarayya da ke Kachia Kudancin Jihar Kaduna wannan shekarar karatu ta bana ce zata fara aiki babu kama hannun yaro na koyar da sabbin dalibanta na farko. Lamarin aikin Likita, koyon hada magunguna, da kuma ma’aikatan kula da lafiya masu aiki da Likita suna daga cikin manyan kwasa- kwasen da aka fi basu matukkar fifiko.
Wannan ya biyo bayan bada takardar shedar mallakar filin da jami’ar take daga hannun gwamnatin Jihar Kaduna zuwa hannun Gwamnatin tarayya.
- Gwamnati Za Ta Goyi Bayan Shirin Fim Kan Tarihin Shekaru 25 Na Dimokuraɗiyyar Nijeriya
- Kasar Sin Na Adawa Da Zarge-Zargen G7 Don Gane Da Tekun Kudancin Kasar
Karamin Ministan ilimi Dakta Maruf Alausa,shi ne wanda ya tabbatar da ci gaban da aka samu a Abuja lokacin da Gwamnan Jihar Uba Sani ya mikawa Ministan satifiket na shedar mallakar fili zuwa ga ita Gwamnatin tarayyar.
Miistan ya ba Gwamna Sani tabbacin cewar duk wadansu lamurran da suka shafi kudi an tabbatar da su domin Jami’ar ta fara aiki ba tare da wata matsala ba.
Ya ce “Jami’ar ko shakka babu za ta fara aiki. Domin tuni ne muka samu amincewar majalisar kasa dangane da ma’aikatan da kuma kudaden da za ayi amfani da su a cikin kasafin kudin shekarar 2025 kamar yadda Dakta Alausa ya kara jaddadawa cikin bayaninsa’’.
Ya kara bayanin cewar Jami’ar za ta dauki sahun dalibanta na farko wato shekarar karatu ta 2025, inda ya kara jaddada aniyar gwamnati ta bada damar samun yin karatu na ilimi mai zurfi tare da bunkasa shi.
Ministan har ila yau ya ce zai taimaka wajen tabbatar da cewar Jami’ar ta samu nata kason daga Hukumar kula da ilimin manyan makaratun ta kasa, domin hakan zai taimakawa bunkasa Jami’ar cikin wani lokaci nan gaba.
Ya ci gaban da bayanin “Zan tabbatar da cewar Jami’ar ta samu taimako na gidauniya kula da ilimi mai zurfi ta lamurran manyan makarantu ta samun kudade daga wurinta wannan shekarar. Don haka wannan rana ce ta farin ciki ga al’ummar Kudancin Kaduna, al’ummar Jihar Kaduna, da kuma al’ummar Nijeriya baki daya kamar yadda ya furta maganar,” .
Da yake an mika satifiket din mallakar filin yanzu Gwamnatin tarayya c eke da mallakin filin da kuma Jami’ar, hakan kuma ya bada wata damar fara aikinta a Hukumance. “Filin yana da hekta fiye da 200 wanda yanzu Gwamnatin Jihar Kaduna ta mallakawa Gwamnatin tarayya ta hanyar ma’aikatar ilimi ta tarayya.Yanzu mune muke da takardar satifiket na mallakar Jami’ar,”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp