Za a gudanar da taron koli kan matan kasa da kasa daga ranar 13 zuwa 14 ga watan Oktoba a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Game da wannan batu, darektar kula da harkokin yankin Asiya da tekun Pasifik na ofishin mata na Majalisar Dinkin Duniya, Christine Arab ta bayyana cewa, taron kolin ya zo daidai lokacin da ya dace!
A ganinta, shekaru 5 kacal suka rage wajen cimma ajandar wanzar da ci gaba mai dorewa ta nan da shekara ta 2030, amma ba a aiwatar da burikan da suka shafi daidaiton jinsi a duk fadin duniya bisa shirin da aka tsara ba. Ta ce kasa da kasa za su iya amfani da taron kolin a wannan karo, wajen tattaunawa kan matakan da suka dace, tare da musayar dabarunsu.
Christine Arab ta kuma ce, tana matukar farin-cikin samun damar halartar taron, inda ta ce, tun daga shekara ta 1995, har zuwa yanzu, Sanarwar Beijing gami da Kundin Matakai suna karfafa mata gwiwar yin aiki. (Murtala Zhang)