Ana sa ran shigar jiragen sama da kasar Sin ke kerawa kasuwannin harkokin sufurin jiragen Afirka zai inganta hanyoyin sadarwa, da rage farashin gudanarwa, da kuma tallafa wa fadada kamfanonin jiragen sama na nahiyar, kamar yadda wani babban jami’in masana’antar ya bayyana a jiya Talata.
Babban sakataren kungiyar kamfanonin jiragen sama na Afrika, wacce take kungiyar kasuwancin kamfanonin sufurin jiragen sama na Afirka da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya, Abderahmane Berthe, ya bayyana a gefen taron kara wa juna sani na inganta zirga-zirgar jiragen sama na Afirka cewa, sashen jiragen sama na kasar Sin yana kera jiragen sama masu inganci sosai, wadanda ke samun karbuwa a duniya.
- Za Mu Bi Doka Domin Dawo Da Haƙƙinmu – Fubara
- Ribas: Fubara Ya Fice Daga Gidan Gwamnati Yayin Da Sabon Shugaba Ke Shirin Karɓar Mulki
Berthe ya kuma bayyana cewa, ya riga ya tattauna a game da rawar da kasar Sin za ta taka a masana’antar sufurin jiragen sama ta Afirka ta hanyar Kamfanin Jiragen Sama na Kasuwanci na Kasar Sin, wato COMAC a takaice.
Ya ce, COMAC ya samar da ingantattun na’urorin zamani a cikin jiragen da yake kerawa, wanda hakan ya sa suka zama sabon zabi da mafita a kan jiragen da ake kerawa a kasashen yammacin duniya.
Taron na kwanaki biyu da aka fara a jiya Talata, ya tara mahalarta sama da 100, da suka hada da jami’ai daga Majalisar Dinkin Duniya, da gwamnatoci, da masu kula da harkokin sufurin jiragen sama, da kuma kamfanonin jiragen sama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp