Shugaban hukumar tsara tattalin arzikin kasar Sin ya bayyana a yau Labara cewa, kasar Sin za ta iya cimma burin ci gaban GDP na kimanin kashi 5 cikin dari da ta sanya gaba a shekarar 2024.
Zheng Shanjie, darektan hukumar raya kasa da garambawul ta kasar Sin, ya shaidawa manema labarai a gefen zaman majalisar wakilan jama’ar kasar da ke ci gaba da gudana a kasar Sin cewa, kasar na da kwarin gwiwa, da iyawa da kuma yanayin da ake bukata na cimma burin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma a bana.
Zheng ya kara da cewa, burin ci gaban tattalin arziki da aka sanya gaba ya dace da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 wato shekarar 2021 zuwa 2025, kuma ya dogara ne kan yuwuwar bunkasuwa da yanayin tattalin arzikin kasar Sin. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp