Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a jiya Litinin cewa, bisa gayyatar Wang Yi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai ziyarci kasar Sin daga ranar 24 zuwa 26 ga wata.
A wannan rana kuma, shugaban sashen kula da harkokin arewacin Amurka da Oceania na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya yi wa manema labarai karin haske game da batun, inda ya ce, yayin ziyarar sakatare Antony Blinken, kasar Sin za ta mai da hankali kan manyan manufofi guda biyar.
- Jakadan Sin Dake Amurka: Ana Fatan Amurka Da Sin Su Bi Hanya Daya Don Binciken Yadda Kulla Abota Tsakaninsu
- Kasar Sin Na Kokarin Samar Da Ruwa Ga Yankunan Dake Fama Da Fari
Da farko dai, fahimtar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Wato kamata ya yi a ba da tabbaci ga huldar dake tsakanin kasar Sin da Amurka don kara kyautata ta, tare da samun bunkasuwa bisa ingantacciyar hanya mai dorewa yadda ya kamata.
Na biyu, ya kamata a kara inganta tattaunawa tsakanin sassan biyu.
Na uku, a daidaita bambance- bambance dake akwai tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata. Ya ce a ko da yaushe, akwai bambance- bambance a tsakanin kasashen biyu, amma hakan ba zai iya mamaye dangantakar dake tsakaninsu ba.
Wato bai kamata Amurka ta rika tabo wasu batutuwa masu tada kura game da kasar Sin ba, wadanda suka shafi Taiwan, dimokuradiyya da hakkin dan Adam, hanyoyi da tsare-tsaren da take bi, da ma ‘yancin samun ci gaba da dai sauransu.
Na hudu, ya kamata a inganta hadin kai irin na samun moriyar juna a tsakanin sassan biyu.
Na biyar, ya kamata kasashen biyu su sauke nauyin dake wuyansu a matsayin manyan kasashe. (Bilkisu Xin)