Wani jami’in yada labarai na babban yankin kasar Sin ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ba za a amince da duk wani mahaluki ko wata runduna da za ta raba yankin Taiwan da kasar Sin ba, kuma babu yadda za a yi a lamunce da ayyukan “ballewar Taiwan” ta ko wace hanya.
Jami’in yada labarun, da ke aiki a ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin, Chen Binhua ya kara da cewa, matukar dakarun ‘yan awaren suka kuskura suka bari tura ta kai bango, za a dauki kwararan matakan mayar da martani a kansu.
- Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya
- Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
Chen ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yin tir da kalaman jagoran ‘yan awaren Taiwan na baya-bayan nan, Lai Ching-te, wanda ya yi ikirarin cewa bangarori biyu na mashigin Taiwan ba su nuna biyayya ga junansu.
Da yake mayar da martani kan haka, Chen ya jaddada cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya rabuwa da shi ba. Kana bai taba zama kasa ba kuma ba zai zama ba a gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp