Bisa gayyatar da gwamnatin jamhuriyar kasar Laberiya ta yi masa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, Bater ya halarci bikin rantsar da shugaba Joseph Nyumah Boakai a jiya Litinin a Monrovia, babban birnin kasar Laberiya. Boakai ya gana da Bater a ranar 21 a birnin.
Bater ya mika gaisuwa da fatan shugaba Xi Jinping ga Boakai, ya kuma bayyana cewa, bangaren Sin na dora muhimmanci sosai kan ci gaban dangantakar kasashen Sin da Laberiya, yana son yin aiki tare da bangaren Laberiya don kara inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban, da kuma sa kaimi ga dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Laberiya don ci gaba da samun sabbin sakamako.
Boakai ya bukaci Bater ya mika gaisuwa da fatansa ga shugaba Xi Jinping. Yana mai cewa, bangaren Laberiya yana mai da hankali sosai kan abokantakar dake tsakanin kasashen Laberiya da Sin, kuma zai tsaya tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak, kuma yana son zurfafawa hadin gwiwa tsakaninsa da kasar Sin a muhimman fannoni kamar manyan kayayyakin more rayuwa da albarkatun mutane, domin kara habaka dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.(Safiyah Ma)