• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’in Yada Labarai: Kasar Sin A Shirye Take Ta Aiwatar Da Hadin Gwiwar Kasashe Na Hakika Tare Da Mambobin G20

by CGTN Hausa and Sulaiman
11 months ago
Sin

A jiya Talata, wani jami’in yada labarai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar na fatan yin hadin gwiwa tare da sauran kasashe mambobin kungiyar G20, domin gudanar da ayyukan hadin gwiwa na hakika. Ya fadi haka ne a yayin da aka tambaye shi karin haske game da jawabin da Shugaba Xi Jinping ya yi a kan sauye-sauyen hukumomin gudanar da harkokin duniya, da ya gabatar a wurin taron kolin G20 da ake gudanarwa a Brazil.

Jami’in yada labarun Lin Jian ya ce, tun daga lokacin da aka kafa kungiyar G20, a ko da yaushe tana fuskantar kalubalen duniya gaba daya, kuma tana kokarin samar da hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya bisa tsarin tuntubar juna da cin gajiyar juna.

  • Xi Jinping Ya Halarci Zaman Rufe Taron Kolin G20 A Rio De Janeiro
  • Xi Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Babban Taron Intanet Na Duniya Na Bana A Wuzhen

A cewar jami’in, a cikin jawabin da Shugaba Xi ya gabatar yayin zama na biyu na taron kolin G20 karo na 19, ya bayyana cewa, akwai bukatar kungiyar G20 ta ci gaba da yin aiki a matsayin wani ginshiki na inganta gudanar da harkokin duniya, da ciyar da tarihi gaba, da samar da babban ra’ayi da kasashen duniya suka cimma matsaya a kai a fannonin tattalin arziki, kudi, cinikayya, fasahar zamani da inganta muhalli, da dai sauransu, a cewar kakakin.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Don haka, ya kamata kungiyar G20 ta karfafa hadin gwiwar tattalin arzikin duniya, da samar da yanayi mai bude kofa, da hada kai, da rashin nuna bambanci ga hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen duniya, da kara yawan fada-a-ji da wakilcin kasashe masu tasowa, da kiyaye tafiyar da kasuwannin hada-hadar kudi na duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Rahoto: Yanayin Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Kasar Sin Na Ci Gaba Da Habaka

Rahoto: Yanayin Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Kasar Sin Na Ci Gaba Da Habaka

LABARAI MASU NASABA

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.