Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na kasa (NEC), ya amince da shugaba Bola Tinubu da ya nemi wa’adi na biyu a shugabancin kasarnan. An yanke wannan shawarar ne a babban taron Jam’iyyar na kasa da aka gudanar a ranar Laraba a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja.
Cikin manyan shugabanni a jam’iyyar wadanda ba su halarci taron ba, sun hada da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da kuma wasu tsofaffin gwamnoni.
- Zan Fice Daga APC Matuƙar Abdullahi Abbas Ya Ci Gaba Da Zama Shugaba A Kano – Ministan Tinubu
- Tinubu Ya Taya Babban Editan LEADERSHIP, Ishiekwene Murnar Cika Shekaru 60
Duk da rashin halartar taron da wasu shugabanni da ba su yi ba, taron ya samu halartar manyan ‘yan Jam’iyyar da suka hada da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da wasu gwamnoni da dama.
Shugaba Tinubu ya bayyana jin dadinsa ga shugabannin jam’iyyar da ‘ya’yan jam’iyyar bisa goyon bayan da suka ba su, inda ya bayyana irin sauye-sauyen da gwamnati ta yi da nasarorin da ta samu wajen karfafa tsaro da samar da abinci.
Taron na (NEC) ya kuma samu halartar shugaban kungiyar gwamnonin (APC), Hope Uzodinma, ya kuma gabatar da kudirin amincewa da shugaban kasa da ya dora da shugabancin kasar a zango na biyu.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci samar da sabon ginin sakatariyar jam’iyyar na kasa, ya kuma bayyana irin kokarin da jam’iyyar ke yi na kula da mambobinta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp