Akwai shirye-shiryen hada jam’iyyun Labour Party (LP) da NNPP don karfafa Jam’iyyun da nufin kayar da Jam’iyyar APC mai mulki.
Kakakin kungiyar tuntuba ta kasa (NCF) da jam’iyyar LP, Dr. Yunusa Tanko ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da gidan talabijin na Arise News.
Da aka tambaye shi cewan, ko akwai shirin hada Peter Obi na jam’iyyar Labour da Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP domin hada karfi da karfe wajen kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023 mai zuwa? Tanko ya ce ba zai iya tabbatar wa ba ko angama cimma matsaya amma dai akwai Shirye-shiryen hakan.
A cewar Tanko, hadewar jam’iyyun biyu, ra’ayi ne da wasu suka bijero da shi, amma muna ganin cewa mai rike da tutar jam’iyyar Labour, Peter Obi, wanda ke da dimbin magoya baya a Kudancin kasar nan yana bukatar hada kai da sauran jama’a wadanda suke da dimbin magoya baya sosai a yankin Arewacin Nijeriya.
Ya kara da cewa, a halin yanzu babu wani rikici a jam’iyyar LP, inda ya ce jam’iyyar tana da karfi a yanzu fiye da yadda take a da.