Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dakta Ajuji Ahmed, ya tabbatar da shugabancinsa, inda ya yi watsi da ikirarin wani bangare na jam’iyyar, inda ya bayyana cewa shi ne wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da shi.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Ahmed ya tabbatar da cewa, jam’iyyar na nan a karkashin shugabancinsa da kuma kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da aka kaddamar a shekarar 2022.
- Sin Ta Yi Watsi Da Tsegumin Da Marco Rubio Ya Yi Kan Hadin Gwiwarta Da Latin Amurka
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum Uku Da Kokon Kan Mutum A Imo
Dakta Ahmed ya jaddada cewa, INEC jam’iyyar NNPP daya ta sani, mai tambarin launin ja, fari, da jajayen kalamai, da littafi, da kuma hular ilimi mai taken, ilimi ga kowa, “Education for All”.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da masu yada labarai da su tabbatar da ikirarinsa da ke shafin hukumar ta INEC.
Da yake martani kan taron da wani bangare na jam’iyya NNPP ya gudanar a Legas kwanan nan, Dr. Ahmed ya yi watsi da taron, a matsayin taron da ya sabawa doka.
Ya bayyana cewa, jam’iyyar bata gudanar da wani taro a wajen hedikwatarta da ke Abuja ba, ya kuma musanta ikirarin kaddamar da sabon kwamitin gudanarwa a wasu wurare sabanin na Abuja.