A ci gaba da ayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da na Kansiloli da ke gudana a Jihar Bauchi a ranar Asabar, Samira Shu’aibu Maikano daga jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) daga gundumar Wandi a ƙaramar hukumar Dass, ta lashe kujerar Kansila.
Ta samu ƙuri’u 1610, a yayin da Bashir Abdullahi daga jam’iyyar PDP ya zo na biyu da ƙuri’u 1352 sai Abdulwahab Aliyu daga APC da ƙuri’u 230.
- Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Sin Da Laos Da Myanmar Da Thailand Sun Gudanar Da Wani Taro
- Ma’aikatar Tsaron Gidan Kasar Sin: Amurka Na Yunkurin Nuna Fin Karfinta Bisa Amfani Da Makamashin Nukiliya
Ana dai cigaba da tattara sakamakon zaben kamar yadda rahotonnin ke zuwa.
Sai dai, wakilinmu ya tabbatar da cewa mafi yawancin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli PDP ce ke lashewa.