Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Uwargida Sarautar Mata.
Yau kuma za mu yi magana kan abin ya shafi Jan Kunne Ga Uwargida.
Uwargida kar ki kasance daga cikin mata masu kyamar uwar mijinsu. Kar ki kuma ki zama daga cikin mata masu wulakanta uwar mijinsu. Kar ki kasance daga cikin mata masu raba uwa da danta.
Ki sani wannan baiwar Allah ta wahala akan wannan mutumin da kika gani har kika aure shi, ba ki san irin wahalar da ta sha ba wajen ganin tarbiyyarsa ta inganta, har ya zama abin da ya zama kika ganshi ya baki sha’awa kika aure shi.
Duk son da namiji zai miki matukar ya ga ba kya son mahaifiyarsa, ba kya girmama ta wannan soyayyar za ta gushe daga zuciyarsa. Saboda duk duniya babu abin da ya fi so ya fi bukata ya fi girmamawa irin mahaifiyarsa, sannan duk wani wanda ba zai girmama masa ita ba ko kuma zai walakanta ta to ba zai iya ganinsa da mutunci ba ko kuma ma zai iya raba alaka da shi.
Tsakanin ki da ita sai ganin kimarta da girmanta, da mutunta ta da kuma girmama ta ki dauke ta tamkar mahaifiyarki, idan kika yi mata haka ke ma za’a yi miki.
Sannan musani duk wanda ya girmama mahaifiyar wani shima za’a girmama tasa kuma duk wanda ya walakanta mahaifiyar wani shima za’a walakanta tasa, don haka uwa ba a bar walakantawa bace koda kuwa ba ita ta haifaiki ba ai tahaifi wani, sannan matar da ta haifar miki mutum kamar miji wanda shi ne jigon rayuwarki, shi ne majubincinki, shi ne mai daukar komai naki na rayuwa to ai kin ga mahaifiyarsa ba ta cancanci walakanci ba a wurinki. Allah ya bamu ikon girmama na gaba da mu.