A ranar Asabar ta makon gobe 19 ga Oktoba, tsohon Shugaban Kasa Janar Yakubu Dan-Yumma “Jack” Gowon zai cika shekara 90 cif a duniya.Â
Janar Yakubu Gowon wanda aka haife shi a kauyen Lur da ke Karamar Hukumar Kanke ta yanzu a Jihar Filato a ranar 19 ga watan Oktoban 1934, dan kabilar Angas (Ngas) ne da mahaifinsa ya kasance na farko-farkon karbar addinin Kirista a Arewa.
- Ba Mijina Ba Ne Sanadin Ƙuncin Rayuwa Da Ake Ciki A Nijeriya – Uwargidan Shugaban Ƙasa
- Yankin Taiwan Na Sin Ba Zai Taba Zama Cikakkiyar Kasa Ba
Wannan ya sa Janar din ya taso a garin Wusasa wani sansanin mabiya addinin Kirista da suka fito daga Arewacin kasar nan da ke wajen birnin Zariya tare da samun iliminsa a Zariya kafin ya shiga aikin soja.
Janar Yakubu Gowon ya samu horon soja a Nijeriya da Ghana da kuma fitacciyar Kwalejin Horar da Hafsoshin Sojoji ta Sandhurst da ke Ingila. Kuma ya yi aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar Kwango har sau biyu a cikin ayarin sojojin Nijeriya a farkon 1960.
Saurayi Ya Zama Shugaban Kasa
Juyin mulkin ranar 15 ga Janairun 1966 ne, ya fara fito da Janar Yakubu Gowon a harkokin mulkin kasar nan, inda aka nada shi Babban Hafsan Sojojin Kasa na Nijeriya a 1966. Sai dai shekarar ba ta kare ba aka nada shi Kwamishinan (Ministan) Harkokin Kasashen Waje, inda ya karbi kujerar daga Alhaji Nuhu Bamalli. Sannan ya zama Kwamishinan (Ministan) Tsaro. Kuma ya zama Shugaban Kasa na mulkin soji yana da shekara 31 kacal a duniya bayan kashe Janar Johnson Aguiyi-Ironsi a wani juyin mulkin da sojojin Arewa suka yi a watan Yulin 1966 don mayar da martani kan juyin mulkin Janairun 1966.
Yadda Matashin Shugaban Kasar Ya Tunkari Yakin Basasa
Jim kadan da hawansa kujerar shugabancin Nijeriya, sai Gwamnan Jihar Gabas na lokacin Kanar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ya ayyana balle yankinsa daga Tarayyar Nijeriya, tare da kafa kasar Biyafara.
Duk da kasancewarsa matashi mai karancin shekaru, Janar Gowon ya fi fifita bukatun kasa a kokarinsa na magance wannan tawaye, inda cikin kankanin lokaci ya dauki kwakkwaran matakin dakile matsalar ‘A Ware’ da ta taso a Arewa, inda aka rika kai hare-hare ga ‘yan kabilar Ibo, wadanda sojojin da suka jagoranci juyin mulkin 1966 suka fito daga cikinsu.
Kuma a kokarin Janar Gowon na kawo karshen rikicin ne a ranar 27 ga watan Mayun 1967 ya raba Nijeriya zuwa jihohi 12, amma duk da haka, kwana uku da bayyana haka, sai Jihar Gabas ta ayyana ballewa daga Nijeriya tare da bayyana kafa kasar Biyafara.
Kasancewar Janar Gowon mutum mai son zaman lafiya da kaunar kasa, ya sa ya umarci sojojin Nijeriya da suke fagen daga suna fafatawa da sojojin Biyafara cewa su tuna suna yaki ne da ‘yan Nijeriya da za a iya shawo kansu su dawo cikin kasar nan. Kuma ya kyale masu sa ido na kasashen duniya su rika sa ido kan yadda sojojinsa suke gudanar da yakin. Sannan bayan samun nasarar sojojin Nijeriya a kan na Biyafara a watan Janairun 1970, sai Janar Gowon ya bayyana wata kalma da ta shiga kundin tarihi, wato ‘Babu wanda ya yi nasara ko wanda aka yi nasara a kansa.’
Shahararsa A Duniya
Janar Gowon ya zama fitaccen jagora a duniya inda ya taka rawa sosai wajen kafa Kungiyar Bunkasa Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma (ECOWAS). Janar Yakubu Gowon ya zama Shugaban Kungiyar Hada Kan Afirka (OAU) wadda yanzu ake kira Tarayyar Afirka (AU) daga watan Mayun 1973 zuwa Yunin 1974.
Kuma yana halartar taron Kungiyar OAU a kasar Uganda ne wasu sojoji a karkashin Janar Murtala Mohammed suka yi masa juyin mulki a ranar 29 ga watan Yulin 1975.
Janar Gowon ya rungumi kaddara kuma ya nemi mafakar siyasa a kasar Birtaniya. Sai dai bayan kashe Janar Murtala a juyin mulkin da bai yi nasara ba 1976, sai aka soke dukkan mukamansa na soja bisa zarginsa da hannu a yunkurin juyin mulkin.
Janar Gowon ya ci gaba da zaman gudun hijira a Ingila inda ya yi neman ilimi har ya yi digirin digirgir a Jami’ar Warwick a 1983. Kafin haka, a 1981, tsohon Shugaban Kasa Shehu Shagari ya yi masa afuwa kan zargin hannunsa a kisan Janar Murtala, wanda hakan ya ba shi damar dawowa Nijeriya.
Kuma a 1987, Shugaban Kasa Janar Ibrahim Babangida ya dawo masa da mukamansa na soja. Sannan Jami’ar Jos ta nada shi Farfesan Kimiyyar Siyasa a tsakiyar shekarun 1980.
Kafin kammala takaitaccen tarihin rayuwar wannan haziki, yana da kyau mai karatu ya san cewa, Janar Buhari ya kasance babban dogarinsa (ADC) a lokacin da yake shugabancin kasa. Yayin da kuma Janar T.Y Danjuma ya kasance Babban Hafasan Sojojin Kasa.
Tsohon Shugaban Kasa mafi dadewa kuma Janar din soja mafi nisan kwana da ke raye, za a ci gaba da girmama Janar Gowon a matsayin dattijon kasa mai kishin kasa da son zaman lafiya da ya bullo da shirye-shirye masu yawa don tabbatar da hadin kan kasa.