Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ya shaki iskar ‘yanci bayan ya shafe kwanaki 56 a hannun ‘yan bindiga.
In ba a manta ba, mun rahoto cewa, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) a mahaifarsa da ke karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 2025.
- Yadda Rasuwar Galadima Abbas Ta Haɗa Kawuna ‘Yan Siyasar Kano Masu Hamayya Da Juna
- Neman “’Yancin Kan Taiwan” Da Jam’iyyar DPP Ke Yi Zai Ci Tura
An yi garkuwa da shi ne tare da wasu mutane mazauna garin, su tara.
Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su.
Ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a kara musu kudin fansa, amma hakan ba ta yi wu ba.
Wata majiya mai tushe ta sojoji ta kuma tabbatar da sakin Tsiga. Majiyoyi na kusa da dangin sun ce yana cikin koshin lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp