A jajiberen sabuwar shekarar 2024 dake tafe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da yanar gizo, don murnar sabuwar shekara.
Ga cikakken jawabin.
‘Yan uwa da abokai, maza da mata, barka dai. Lokacin sanyi na dab da wucewa, an fara shiga lokacin dumi yanzu. A jajiberen sabuwar shekara ta 2024, daga nan Beijing ina muku barka da sabuwar shekara.
A shekarar 2023 da muka yi ban kwana da ita, mun yi kokari sosai, mun samu ci gaba bayan mun jure wahalhalu. Wasu kyawawan abubuwa sun wakana a zaman rayuwarmu, yayin da muka samu sakamako da dama. Duk da cewa mun gamu da wasu matsaloli a wannan shekarar da muke ciki, amma mun nuna karfin hali wajen samu makoma mai kyau.
A wannan shekara, mun samu ci gaba mai inganci. Mun kyautata matakan dakile da kandagarkin cutar numfashi ta COVID-19 yadda ya kamata. Tattalin arzikin kasarmu ya farfado, ana kuma gudanar da aikin raya kasa mai inganci. Tsarin masana’antunmu ya kara kyautatuwa, yayin da sabbin muhimman masana’antu na zamani marasa gurbata muhalli suka samu saurin ci gaba. Haka kuma kasarmu ta yi shekaru 20 a jere tana yin girbin hatsi. Muhallin yanayi ya kyautata matuka a kasar Sin, yayin da ake farfado da yankunan karkara. An bude wani sabon babi na farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin. Saurin ci gaban sabon yankin Xiong’an ya wuce yadda ake tsammani.
Yankin tattalin arziki na kogin Yangtze ya bunkasa yayin da babban yankin Greater Bay na Guangdong, Hong Kong da Macao ya ba da jagora wajen samun ci gaba. Kasar Sin ta kara karfin tattalin arzikinta duk da matsaloli da dama da aka fuskanta.
A wannan shekara, mun samu ci gaba mai karfi. Bayan kokari na dogon lokaci, karfin kirkire-kirkire da na bunkasuwa sun samu babban ci gaba. An fara amfani da babban jirgin saman fasinja samfurin C919 a kasuwar jigilar fasinjoji. Babban jirgin ruwan fasinjoji da kasar Sin ta kera da kanta, ya gudanar da zirga-zirgar gwaji cikin nasara.
An samu nasarar sauya ayyukan kumbunan Shenzhou a sararin samaniya, baya ga yadda jirgin da ke tafiya a karkashin ruwa kirar Fendouzhe ya samu nasarar zuwa teku mai matukar zurfi. Ban da wannan kuma, kayayyaki kirar kasar Sin sun samu karbuwa, har ma ba a iya sayen sabbin wayoyin salula kirar kasar Sin cikin sauki a kasuwanni.
Motoci masu amfani da wutar lantarki, batir iri na Lithium, kayayyaki masu amfani da karfin hasken rana, dukkansu sun shaida ci gaban sha’anin kere-kere na kasar Sin. Bisa ruhin Sinawa na dogaro bisa karfin kansu da dagewa wajen yin wani abu, kasar Sin ta samu manyan sabbin kirkire-kirkire.
A cikin wannan shekara, mun samu ci gaba mai cike da kuzari. An samu nasarar shirya gasar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’in kasa da kasa ta birnin Chengdu, da gasar wasannin motsa jiki ta kasashen Asiya ta birnin Hangzhou, inda ‘yan wasanni na kasar Sin suka lashe lambobin yabo da yawa. Haka kuma an samu yawan masu yawon shakatawa a lokutan hutu, kasuwar fina-finai ma ta samu bunkasuwa, gasannin wasannin kwallon kafa da na kwando da aka yi a kauyuka sun samu karbuwa. Yanzu al’ummar Sinawa sun saba da salon zaman rayuwa maras gurbata muhalli. Yadda suke jin dadin zaman rayuwa, da fama da ayyuka ya nuna kokarin al’ummar kasarmu na neman zama mai dadi, da kasar Sin da ke cike da kuzari.
A cikin wannan shekara, mun samu ci gaba mai karfafa imani. Sin kasa ce mai girma, wadda ke da wayewar kai mai dogon tarihi. A kan wannan kasa mai fadin kasa, da hamada, kananan koguna, rawayen kogi, kogin Yangtze, dukkansu sun shaida tarihin al’ummar Sinawa na dubban shekaru, da kishin kasar da al’ummarta ke da shi. Asalin wayewar kan al’ummar Sinawa da aka gano a garin Liangzhu da garin Erlitou, kalmomin Sinanci kan kashi da bawon kunkuru da aka gano a Yinxu, kayayyakin tarihi da aka gano a Sanxingdui, da babban dakin adana littattafan da aka yi musu bambancin dab’i na kasar, dukkansu abubuwan shaidu ne na dogon tarihi da wayewar kan kasar Sin. Wannan zai ba mu cikakken imani da karfi.
Baya ga kokarin kasar Sin na raya kanta, tana kuma rungumar kasa da kasa da hannu bibbiyu, tare da sauke nauyin dake kanta.
Mun samu nasarar gudanar da taron koli tsakanin kasar Sin da kasashen yankin Tsakiyar Asiya, taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya. Baki daga sassa daban daban na duniya sun halarci tarurruka a jere da aka gudanar a kasar Sin. Ni ma na ziyarci wasu kasashe da kuma halartar tarukan kasa da kasa da dama, tare da ganawa da tsoffi da sabbin abokai, inda na bayyana ra’ayin kasar Sin da zurfafa ra’ayin bai daya da ke tsakaninmu. Duniya tana sauyawa ko da yaushe, amma har kullum neman ci gaba cikin lumana, ita ce babbar hanyar da ta kamata a bi. Haka kuma samun nasara tare cikin hadin gwiwa, ita ce manufar da ta kamata a bi.
A kan hanyarmu ta samun ci gaba, mu kan gamu da matsaloli. Wasu kamfanoni na fuskantar matsin lamba wajen tafiyar da harkokinsu, yayin da wasu mutane kuma suka gamu da matsalar samun aikin yi, da zaman rayuwarsu. Sanin kowa ne cewa, an yi ambaliyar ruwa, mahaukaciyar guguwa, girgizar kasa da sauran bala’u daga indallahi a wasu sassan Sin, wadanda suka kada min zuciya sosai. Duk da haka, mutanenmu ba su ji tsoro ba, sun taimakawa juna, sun daidaita matsalolin da suke fuskanta, sun jure wahala, wannan ya burge ni matuka.
Manoman da suke fama da aiki a gonaki, ma’aikatan da suke aiki tukuru, ‘yan kasuwan da suke kokarin raya sha’aninsu, sojojin da suke tsaron kasa, da duk wadanda suke gudanar da ayyukansu sun sauke nauyin dake bisa wuyansu. Kowa da kowa ya ba da nasa gudummawa. Har kullum al’ummar Sinawa, abin dogara ne wajen jure wahalhalu.
Badi, za a cika shekaru 75 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. Za mu tsaya tsayin daka kan zamanantarwa mai salon kasar Sin, da aiwatar da cikakken sabon tunanin raya kasa daidai daga dukkan fannoni, da gaggauta kafa sabon tsarin raya kasa, da kara azama kan samun ci gaba mai inganci, da kuma daidaita batutuwan ci gaba da tsaron kasa yadda ya kamata. Har ila yau, za mu tsaya tsayin daka kan neman ci gaba ba tare da tangarda ba, da neman kwanciyar hankali ta hanyar samun ci gaba, da yin watsi da tsoffin batutuwa da rungumar sabbi, da inganta da karfafa farfadowar tattalin arziki, da tabbatar da tafiyar tattalin arziki ba tare da wata matsala ba. Haka zalika za mu zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, da karfafa aniyar farfado da ci gaban kasa, da kara kuzari kan tattalin arziki, da kara karfin ba da ilmi, bunkasa kimiyya da fasaha, da horar da kwararru. Za mu ci gaba da goyon bayan yankunan Hong Kong da Macao ta yadda za su yada fifikonsu da kiyaye dawamammen wadata da kwanciyar hankali yayin da aka shigar da su cikin baki dayan bunkasar kasarmu ta Sin. Tabbas za mu dinke kasarmu waje guda. ‘Yan uwanmu na gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan za mu hada hannunmu da zuciya daya, a kokarin samun farfadowar al’ummar Sinawa tare.
Muna da babban burin da muke fatan cimmawa, burin da ke shafar kowa, wato za mu yi kokarin ganin al’ummar Sinawa na kara jin dadin zaman rayuwarsu. Ba wa kananan yara ilmi, samar wa matasa aikin yi don su samu nasara, ba wa tsoffi jinya da kulawa, dukkansu muhimman batutuwa ne dake shafar ko wane iyali, kuma harkokin kasa ne, wadanda wajibi ne kowa da kowa ya ba da tasa gudummawa, don gudanar da su yadda ya kamata. Yanzu ana fama da aiki da zaman rayuwar yau da kullum. Ana fuskantar matsin lamba a wajen aiki da ma zaman rayuwa. Wajibi ne mu kiyaye yanayi mai kyau da zaman tare a zamantakewar al’ummar kasa, mu samar da yanayi mai kuzari da damawa da kowa wajen yin kirkire-kirkire, mu kuma saukaka zaman rayuwarmu ta yadda kowa zai ji dadi da farin ciki, ta yadda za mu samu nasara da cimma burinmu.
Yanzu haka ana yake-yake a wasu sassan duniya. Al’ummar Sinawa na dora matukar muhimmanci kan zaman lafiya. Muna fatan za mu hada kai da daukacin kasashen duniya. Ya kamata mu yi la’akari kan makoma da jin dadin dan Adam. Ya kamata mu kara azama kan raya kyakkyawar makomar bai daya ta bil Adama da kafa duniyarmu da kowa zai ji dadin zama a cikinta.
A daidai wannan lokaci, da dare ya yi, kowa ya koma gida. Muna yi wa kasarmu ta Sin fatan samun wadata da ci gaba, kana duniyarmu ta samu kwanciyar hankali da zaman lafiya. Ina yi wa kowa fatan samun alheri da koshin lafiya.
Na gode! (Mai fassarawa: Kande & Tasallah)