Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ‘‘yan wasan ƙwallon ƙafa da ƙwallon kwando mata na Nijeriya man’yan kyautuka da suka haɗa da kuɗaɗe, gidaje da kuma lambobin yabo na ƙasa, biyo ba’yan nasarar da suka samu a mabanbantan gasannin da suka buga, tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya ta doke masu masaukin baƙi Moroko da ci 3-2 a wasan ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Nahiyar Afirika, hakazalika tawagar ƙwallon kwando ta mata ta doke ƙasar Mali da ci 78-64 domin lashe gasar ƙwallon kwando ta ƙasashen nahiyar Afirika karo na bakwai kuma karo na biyar a jere a karo na biyar a jere a birnin Abidjan na ƙasar Cote d’Iɓoire.
A mabanbantan liyafar karrama su da aka guɗanar a fadar shugaban ƙasa dake Presidential Ɓilla an karrama ‘‘yan wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya da gidaje, lambar girmamawa ta MON da kuma zunzurutun kuɗi har Dala 100,000, jerin ‘yan wasan Nijeriya da suka rabauta da wannan kyauta su ne
- Nijeriya Ta Horar Da Likitoci 360 Don Magance Mutuwar Mata Masu Juna Biyu
- Gwamnatin Kaduna Ta Amince Da Hutun Wata 6 Ga Mata Masu Shayarwa
Masu Tsaron Raga
Tochukwu Oluehi. Chiamaka Nnadozie. ‘yan Wasan Baya. Ashleigh Plumptre
Blessing Demehin. Osinachi Ohale. Michelle Alozie. Sikiratu Isa, Shukurat Oladipo
Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun.
‘Yan Wasan Tsakiya
Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini,
‘Yan Wasan Gaba
Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo
Ifeoma Onumonu,
Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar yabo ta ƙasa ga kowace ‘yar wasa ta tawagar ƙwallon kwando a tawagar, tare da ba su kyautar gida a Abuja, a lokacin da yake jawabi ga tawagar, Shettima ya ce nasarar da suka samu alama ce ta ƙarfin haɗin kai.
“Wannan nasara ta nuna abin da ke faruwa iɗan muka yi aiki tare, matan Nijeriya ba su tama bamu kunya a ɓangaren wasanni ba, kuma D’Tigress ta sake sanya mu alfahari,” in ji shi.
D’Tigress kamar yadda ake kiran tawagar ta ƙwallon kwando, ‘yanzu sun tabbatar da samuwar kofinsu na biyar a jere, ta samu nasarar lashe kofin a shekarun 2017, 2019, 2021, 2023, da 2025, wani abin da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin ƙwallon kwando na matan Afirka.
Jerin ‘yan wasan ƙwallon kwando da suka rabauta da kyautar Dala 100,000
Amy Okonkwo, Pallas Kunaiyi-Akpanah, Elizabeth Balogun, Sarah Ogoke, Ifunanya Okoro, Promise Amukamara, Ɓera Ojenuwa, Murjanatu Musa, Blessin Ejiofor, Ezinne Kalu, Ɓictoria Macaulay, Nicole Enabosi.
Masu Horarwa
Rena Wakama, Wani Muganguzi, Prince Oyoyo, Ezeala
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp