Jerin sunayen sabbin jihohi 31 da aka bai wa majalisar dokokin Nijeriya shawarwarin ƙirƙira.
AREWA TA TSAKIYA
1. Jihar Benue Ala daga Jihar Benue ta yanzu.
2. Jihar Okun daga Jihar Kogi ta yanzu.
3. Jihar Okura daga Jihar Kogi ta yanzu.
4. Jihar Confluence daga Jihar Kogi ta yanzu.
5. Jihar Apa-Agba daga Yankin Sanatan Kudancin Benue.
6. Jihar Apa daga Jihar Benue ta yanzu.
7. Jiha ta 37, wato Babban Birnin Tarayya, Abuja.
AREWA-MASO-GABAS
8. Jihar Amana daga Jihar Adamawa ta yanzu.
9. Jihar Katagum daga Jihar Bauchi ta yanzu.
10. Jihar Savannah daga Jihar Borno ta yanzu.
11. Jihar Muri daga Jihar Taraba ta yanzu.
AREWA-MASO-YAMMA
12. Jihar New Kaduna da Gurara daga Jihar Kaduna ta yanzu.
13. Jihar Tiga daga Jihar Kano ta yanzu.
14. Jihar Kainji daga Jihar Kebbi ta yanzu.
15. Jihar Ghari daga Jihar Kano ta yanzu.
KUDU-MASO-GABAS
16. Jihar Etiti a matsayin jiha ta shida a yankin Kudu-Maso-Gabas.
17. Jihar Adada daga Jihar Enugu ta yanzu.
18. Jihar Urashi a matsayin jiha ta shida a yankin Kudu-Maso-Gabas.
19. Jihar Orlu daga Yankin Kudu-Maso-Gabas
20. Jihar Aba daga Yankin Kudu-Maso-Gabas
KUDU-MASO-KUDU
21. Jihar Ogoja daga Jihar Cross River ta yanzu.
22. Jihar Warri daga Jihar Delta ta yanzu.
23. Jihar Bori daga Jihar Rivers ta yanzu.
24. Jihar Obolo daga Jihohin Rivers da Akwa Ibom.
KUDU-MASO-YAMMA
25. Jihar Toru-Ebe daga Jihohin Delta, Edo, da Ondo.
26. Jihar Ibadan daga Jihar Oyo ta yanzu.
27. Jihar Lagoon daga Jihar Legas ta yanzu.
28. Jihar Ijebu daga Jihar Ogun ta yanzu.
29. Jihar Lagoon daga Jihohin Legas da Ogun.
30. Jihar Ibadan daga Jihar Oyo ta yanzu.
31. Jihohin Oke-Ogun da Ife-Ijesha daga Jihohin Ogun, Oyo, da Osun.
Kwamitin bitar Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya karɓi shawarwari domin samar da waɗannan sabbin jihohi da ƙananan hukumomi.