Kyaftin din Argentina, Lionel Messi, mai shekara 35 mai buga gasar kofin duniya karo na biyar ya yi bajinta a wasan da aka yi a filin wasa na Lusai, inda ya zura kwallo a raga sannan ya taimaka aka zura guda daya a wasan da Argentina ta doke Crotia da ci 3-0 a wasan kusa dana karshe na gasar cin kofin duniya.
Dan kwallon da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain ya buga wasa na 25 a gasar kofin duniya, kuma hakan ya sa yanzu ya yi kan-kan-kan da tsohon dan wasan Jamus, Lothar Matthaus.
Haka kuma ya yi kan-kan-kan da tsohon dan wasan Argentina, Gabriel Batistuta a yawan ci wa Argentina kwallaye a kofin duniya masu goma-goma a raga, sannan ya karya tarihin Diego Maradona mai tarihin bayar da kwallo sau takwas ana zurawa a raga, bayan da Messi ke da bakwai.
Matthaus ya buga wa tawagar Jamus dukkan gasar cin kofin duniya tun daga 1982 zuwa 1998 kuma Messi zai kafa tarihin yawan buga wasanni a gasar kofin duniya a wasan karshe da Argentina za ta buga.
Messi ya kusan daukar kofin duniya a 2014, inda suka buga wasan karshe da Jamus ta yi nasara da ci 1-0 a karin lokaci. Kawo yanzu Messi ya ci kwallo 10 a fafatawa 24 da ya buga a dukkan kofin duniya da ya halarta, yana cikin na takwas a jerin wadanda suka ci kwallaye da yawa a gasar kofin duniya.
Miroslab Klose shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a karawa 24 da ya yi gasar kofin duniya, wanda yake da 16 a raga kuma Argentina tana da kofin duniya biyu, amma na karshe da ta dauka shi ne a shekarar 1986 tare da Diego Maradona.
- Lothar Matthaus 25
- Lionel Messi 24
- Miroslab Klose 24
- Paolo Maldini 23
- Cristiano Ronaldo 21
- Diego Maradona 21
- Uwe Seeler 21
- Wladyslaw Zmuda 21.