Shugabar Deloitte na kasar Sin Jiang Ying, ta bayyana a yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wannan mako cewa, a matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar tattalin arzikin duniya.
Haka zalika, a jawabin da ta gabata a wajen taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya (WEF) a birnin Davos na kasar Switzerland, da zai gudana tun daga ranar 15 zuwa 19 ga wata, Jiang ta bayyana cewa, kasar Sin za ta iya samar da karin damammaki ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da samar da guraben ayyukan yi ta hanyar kara bude kasuwanninta, da inganta kasuwanci da zuba jari a duniya.
Ta ce, manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa na kasar Sin, irin su “shawarar ziri daya da hanya daya”, na taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi a kasashen dake raya shawarar.
A ganin Jiang, kasar Sin ba wai kawai tana taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arzikin duniya da cinikayya ba, har ma da samar da zaman lafiya a duniya. (Ibrahim Yaya)