Gamayyar wasu malamai da limamai a Jihar Kaduna a karkashin kungiyar Izala (JIBWIS) sun mika wata takardar korafi ga gwamnatin jihar ta hannun Ofishin Kula da Harkokin Addinai, kan abin da suka bayyana a matsayin yunkurin tada husuma da wasu malamai biyu ke yi – Sheikh Mansur Imam da Malam Imam Ɗangungun.
A cikin takardar korafin da suka sanya hannu kai tsaye, kungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda waɗannan malamai ke yaɗa karatuttuka da maganganun da ka iya jefa al’umma cikin ruɗani da rashin zaman lafiya, musamman a cikin al’ummar musulmi a jihar.
- Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal
- Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260
Wadannan malamai sun bukaci gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakin da ya dace domin hana irin wadannan kalamai da ayyuka da ka iya haddasa rikice-rikice na addini ko kabilanci.
A zantawarsa da manema labarai, jagoran tafiyar Shelkh Umar Shehu Zaria wanda kuma shi ne, babban limamin Masallacin Mus’ab Ibn Umair, Sun jaddada cewa, su ba su da wani buri na daban face ganin an samu zaman lafiya, hadin kai, da mutunta juna a tsakanin mabiya addinai da jama’ar Kaduna baki daya.

“Wadannan malamai guda biyu suna fakewa da malunta suna cin mutunci Manzon Allah SAW. Da’awarsu a Kaduna barazana ce ga zaman lafiya, saboda fitina a jihar Kaduna ba za ta haifar da abu mai kyau ba,” inji shi
Ofishin kula da harkokin addinai karkashin jagoranci Malam Tahir Umar Tahir, ya karɓi takardar korafin kuma ya tabbatar da cewa, zai gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin da kuma daukar matakin da ya dace bisa doka.














