Adadin jigilar fasinjoji da jiragen kasa masu zirga zirga cikin biranen kasar Sin suka yi a shekarar 2024, ya karu da kimanin biliyan 2.8 ko kuma kaso 9.5 a kan na shekarar 2023.
A cewar ma’aikatar kula da sufuri ta kasar, a baran, jimilar jigilar fasinjoji da jiragen suka yi ya kai biliyan 32.24.
Zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2024, tsawon tafiyar da jirage 325 suka yi a fadin birane 54 na kasar Sin, ya kai kilomita 10,945. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)