ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jihar Kaduna Za Ta Ƙarfafa Ƙawancen Tattalin Arziki Da Ƙasar Jamus

by Sulaiman
2 years ago
Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna da gwamnatin kasar Jamus za su kula alaka mai karfi ta fuskar tattalin arziki don samar da ci gaba mai dorewa a jihar.

In ba a manta ba, a watan Disambar 2023, Gwamna Uba Sani ya ziyarci Hukumar Haɗin kai ta Jamus (GIZ) a kokarin Gwamnan na janyo masu zuba jari a jihar Kaduna don ganin jihar a karkashin gwamnatinsa ta samu daukaka da habbaka mai dorewa.

  • Juyin Mulki: Rufe Iyakar Nijeriya Da Nijar Ya Jefa Arewa Cikin Tsaka Mai Wuya – Aliero
  • Gwamnatin Kaduna Za Ta Sa Kafar Wando Da Masu Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba

Sakamakon wannan ziyara, GIZ ta bayyana shirinta na marawa jihar baya domin cimma burinta na ci gaba.

ADVERTISEMENT

A ranar 16 ga watan Janairu, wakilai daga GIZ, karkashin jagorancin Daraktanta, Dr. Markus Wagner, ta kawo wa gwamnatin jihar Kaduna ziyarar kwanaki biyu. Makasudin ziyarar dai ita ce tattaunawa da karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu.

LABARAI MASU NASABA

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

KadunaTawagar GIZ ta samu kyakkyawar tarba daga Gwamna Uba Sani da wasu manyan jami’an gwamnati, inda daga baya aka gudanar da liyafar cin abinci don kara karfafa dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu.

A yayin tattaunawar wadda aka ci gaba a washegari, mataimakiyar gwamna Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ta jagoranci manyan jami’an gwamnati wajen tattaunawa kan wasu bangarori da jihar ke bukatar tallafi daga gwamnatin Jamus. Waɗannan muhimman bangarori sun haɗa da fannin makamashi, samar da sauyi a fannin zamani (dijital), haɓaka saka hannun jari, da noma.

Dr. Wagner ya nuna jin dadinsa da irin karramawar da aka yi masa, ya kuma kara jaddada aniyar GIZ na tallafawa jihar Kaduna wajen samun ci gaba mai dorewa da samar da ayyukan yi.

Mataimakiyar Gwamnan, a madadin gwamnatin jihar, ta godewa GIZ bisa hadin gwiwar da suka yi, tare da ba su tabbacin jajircewar jihar wajen yin amfani da wannan hadin gwiwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Coas
Manyan Labarai

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina
Manyan Labarai

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

November 11, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP
Manyan Labarai

Kotu Ta Sake Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta Na Ƙasa

November 11, 2025
Next Post
Kambun AFCON 2023: Babu Makawa Super Eagles Ta Doke Ivory Coast – Mikel Obi

Kambun AFCON 2023: Babu Makawa Super Eagles Ta Doke Ivory Coast - Mikel Obi

LABARAI MASU NASABA

Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

November 11, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

November 11, 2025
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

November 11, 2025
CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

November 11, 2025
Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.