Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa, jiharsa ce za ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Kaduna a cibiyar koyar da dabarun aikin kwadago ta Michael Imodu wajen taron karawa juna sani wanda aka shirya wa kungiyar kwadago ta Nijeriya, NLC reshen jihar Kano da sauran kungiyo kan dabarun sulhu ga mabanbanta ra’ayi.
- Ya Dace Matasa Su San Illar Da Ke Tattare Da Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba -Pate
- Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan $1.5 Sakamakon Yin Bahaya A Fili
Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar Kano, Abdullahi Musa, ya tabbatar da cewa, jiharsa ce za ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi.
A farkon watan Agustan 2024, Gwamna Yusuf ya kaddamar da kwamitin ba da shawara kan aiwatar da sabon mafi karancin albashi a jihar Kano.