Majalisar tsaro ta jihar Kano ta ayyana kwacen waya a matsayin fashi da makami, kuma duk wani mutum ko kungiyar da aka kama da aikata laifin za ayi masa hukunci da laifin aikata fashi da makami.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida – mai barin gado, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa, majalisar zartaswar jihar, karkashin jagorancin gwamna mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje a yayin zamanta na bankwana a majalisar, ta bayyana cewa, yawaitar kwacen wayoyi a ‘yan kwanakin nan ya kai wani matsayi mai cike da damuwa, don haka, ana bukatar daukar tsauraran matakai.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da samar da wata tawaga ta musamman ta jami’an tsaro domin yaki da masu kwacen wayoyin da suka addabi mazauna jihar.