Gwamnatin jihar Kogi ta amince da fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 72,500 ga ma’aikatan jihar da ma’aikatan kananan hukumomi.
Gwamna Usman Ododo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karbar rahoton kwamitin mafi karancin albashi na jihar a dakin liyafa na gidan gwamnati da ke Lokoja a ranar Litinin.
- Kudin Ajiyar Sin Na Ketare Ya Karu Da Kaso 0.86 Cikin Satumba
- Ma’aikatan NAFDAC Sun Tsunduma Yajin Aiki
An dorawa kwamitin alhakin binciken yadda za a aiwatar da sabon albashin ma’aikata a jihar biyo bayan amincewar gwamnatin tarayya na fara biyan sabon mafi karancin albashi.
Gwamna Ododo ya jaddada cewa, wannan amincewar ta biyan mafi karancin albashi za ta shafi dukkanin ma’aikatan jihar, inda ya ce wannan matakin ya cika alkawarin da gwamnatinsa ta dauka na yi wa jama’a hidima.
Ya bukaci ma’aikatan gwamnati da su ba da himma sosai ga manufofin gwamnatinsa na kawo sauyi a jihar.