Shugaban hukumar gudanarwar jihar Tibet ta kasar Sin Yan Jinhai ya ce, jihar mai cin gashin kanta dake kudu maso yammacin kasar Sin, ta cimma manyan nasarori, a fannin kawar da iskar carbon mai dumama yanayi, matakin da ya ba da babbar gudummawa ga manufofin Sin guda biyu, masu nasaba da shawo kan kalubalen fitar da iskar carbon.
Yan ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi a birnin Nyingchi, yayin bikin bude taron karawa juna sani game da yanayin muhallin halittu na tuddan Qinghai-Tibet, mai lakabin “Namjagbarwa”, wanda ya maida hankali ga gina yankin kasa mai ci gaban muhallin halittu a jihar Tibet.
A cewar kwararru mahalarta taron, yanzu haka a duk shekara, yankin muhallin halittu na tuddan Qinghai-Tibet, yana kawar da tan miliyan 162 na iskar carbon, adadin da ya kai kaso 8 zuwa 16 bisa dari, na jimillar iskar carbon da yankunan Sin ke kawarwa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp