Gwamnatin Jihar Yobe ta bukaci al’ummar jihar su dauki matakan kauce wa ibtila’in ambaliyar ruwa kamar yadda hukumomin kula da yanayi a Nijeriya (NIMET) da takwararta ta ‘Hydrological Serbices Agency (NIHSA)’ suka yi hasashen cewa Jihar Yobe tana daya daga cikin jihohi 32 a kasar nan wadanda ake tsammanin za su fuskanci ambaliyar ruwa a kwanaki uku masu zuwa.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mai taimaka wa Gwamna Mai Mala Buni a fannin yada labaru na zamani tare da dabarun sadarwa, Yusuf Ali, inda ya fara da bayyana cewa wadannan hukumomi suka sanar da cewa za a tika ruwan wanda hasashen ya nuna da yuwa samun ambaliya a jihohin Yobe, Sakwato, Zamfara, Katsina, Kaduna, Kano, Jigawa da Bauchi.
Sauran sun hada da Gombe, Kebbi, Neja, Babban Birnin Tarayya na Abuja, Filato Adamawa, Taraba, Kwara, Oyo, Legas, Ondo, da Ogun. Haka abin zai kasance a Edo, Delta, Bayelsa, Kuros Ribas, Akwa Ibom, Benuwe, Inugu, Ebonyi, Imo, Anambra, Abia da Ribas.
Bugu da kari kuma ya ce, wadannan hukumomin sun ja hankali da cewa ambaliyar zai iya shafar gidajen al’umma, gonaki, hanyoyi da gadoji.
Ya yi karin haske da cewa, bayan wannan hasashe da hukumomi suka yi, yana da muhimmanci jama’a su dauki ingantaccen mataki, musamman al’ummar Jihar Yobe dangane da sakamakon da zai biyo bayan ambaliyar ruwan, wanda ya zo ta dalilin sauyin yanayin da aka samu a wannan shekara.
A hannu guda kuma ya yi kira ga kwamitocin kula da tsabtace muhalli a kananan hukumomi hadi da kungiyoyin taimakon kai da kai, cewa su fadakar da mambobin su wajen ci gaba a aikin tsabtace muhalli ta hanyar yashe magudanun ruwa da gyara hanyoyin ruwa da dakatar da jama’a yin gini kan hanyar ruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp