Ɗaya daga cikin mamallakan Manchester United, Sir Jim Ratcliffe, ya ce zai iya barin kulob ɗin idan magoya bayan ƙungiyar suka ci gaba da cin zarafinsa kamar yadda suka yi wa iyalan Glazer.
Jim Ratcliffe, mai shekaru 72, ya sayi kashi 28.9 na hannun jarin Manchester United a shekarar da ta gabata da kuɗin da ya kai fam biliyan 1.3.
- Kalaman Lai Chin-te Na Shan Suka A Fadin Taiwan
- ’Yan Adawa Na Kitsa Makarkashiyar Tsige Ni – Akpabio
Wannan yarjejeniya ta bai wa kamfaninsa, Ineos, ikon tafiyar da harkokin ƙwallon ƙafa a kulob ɗin.
A wata hira da ya yi da Sunday Times, Ratcliffe ya ce bai damu da zama wanda ba a san shi ba.
A watan da ya gabata, an tabbatar da cewa kulob ɗin zai sake sallamar kusan ma’aikata 200, bayan da aka kori mutum 250 a bara.
A ranar Litinin, Ratcliffe ya shaida wa BBC cewa wasu daga cikin ‘yan wasan Manchester United ba su da ƙwarewa, amma ana biyansu albashi mai yawa fiye da yadda ya dace.
Ya kuma bayyana shirin gina sabon filin wasa mai tsadar Yuro biliyan 2, wanda zai iya ɗaukar mutum 100,000 idan aka kammala.
A ‘yan kwanakin nan, magoya bayan Manchester United sun ci gaba da nuna fushinsu kan iyalan Glazer, masu mallakar sama da kashi 70 na kulob ɗin.
Har ila yau, Ratcliffe bai samu cikakken goyon baya daga ma’aikatan ƙungiyar ba tun bayan zuwansa a shekarar da ta gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp